Shin Netanyahu yana raye ko ya mutu? Matarsa, Sara ta fitar da Sabon Bayani game da jita-jitan da ake yadawa kan mijinta.

Shin Netanyahu yana raye ko ya mutu?

Shin Netanyahu yana raye ko ya mutu? 
Matarsa, Sara ta fitar da Sabon Bayani game da jita-jitan da ake yadawa kan mijinta.

Matar Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, wato Sara Netanyahu, ta bayyana cewa mijinta yana cikin koshin lafiya kuma yana ci gaba da gudanar da aikinsa duk da rikicin yaƙi da ke ƙara tsananta tsakanin Isra’ila da Iran.

Sara Netanyahu ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafukan sada zumunta, inda ta ce goyon bayan jama’ar Isra’ila na ba firaministan ƙarfi a wannan lokaci mai wahala.

Ta ce, “Goyon bayan da muke samu daga jama’a yana ba mu ƙarfi. Firaminista yana ci gaba da aiki ba dare ba rana domin kare ƙasar Isra’ila.”

Wannan bayani ya zo ne bayan jita-jita da suka bazu a kafafen sada zumunta cewa firaministan ya ɓoye ko kuma wani abu ya same shi sakamakon rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai rahotanni daga gwamnati da kuma bidiyoyin da aka fitar sun nuna cewa Netanyahu yana nan da rai, yana kuma halartar tarurrukan tsaro tare da manyan jami’an gwamnati da na soji domin tattauna matakan da za a ɗauka kan rikicin da ke tsakaninsu da Iran.

Rikicin dai ya ƙara tsananta a makonnin nan bayan musayar hare-haren soji tsakanin Isra’ila da Iran, lamarin da ya janyo hankalin ƙasashen duniya tare da ƙara fargabar bazuwar yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: