Rundunar juyin juya halin Musuluncin ƙasar Iran, IRGC Ta Yi Barazanar Kashe Netanyahu Idan Har Yana Raye.

Rundunar juyin juya halin Musuluncin ƙasar Iran, IRGC Ta Yi Barazanar Kashe Netanyahu Idan Har Yana Raye.

Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran, wato (IRGC), ta bayyana cewa za ta ci gaba da nema tare da kashe Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu idan har yana raye.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana Netanyahu a matsayin “mai laifi kuma mai kashe yara,” tana mai jaddada cewa ba za ta daina binsa ba muddin yana raye.

Sanarwar ta fito ne bayan jita-jitar da ta bazu a kafafen sada zumunta da wasu kafofin watsa labarai cewa mai yiwuwa Netanyahu ba ya raye. Sai dai hukumomin Isra’ila sun musanta wannan rahoto, inda suka tabbatar da cewa firaministan yana cikin koshin lafiya.

IRGC ta ce hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a yankuna daban-daban na Gabas ta Tsakiya, musamman wadanda suka jawo asarar rayukan fararen hula, su ne suka kara tsananta rikicin tsakanin kasashen biyu.

Rundunar ta kara da cewa idan aka tabbatar Netanyahu yana raye, za ta ci gaba da farautarsa har sai ta dauki matakin da ya dace a kansa.

Rikicin tsakanin Iran da Isra’ila na ci gaba da kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ke janyo damuwa daga kasashen duniya kan yiwuwar fadada yakin zuwa manyan kasashe a yankin.

News Translation in English Language.

IRGC Threatens to Kill Netanyahu If He Is Still Alive.

Iran’s Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) has threatened to continue pursuing and killing Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu if he is still alive.

In a statement, the Islamic Revolutionary Guard Corps described Benjamin Netanyahu as a “criminal and child killer,” stressing that it will not stop pursuing him as long as he remains alive.

The statement comes amid widespread rumors circulating on social media and some media outlets suggesting that Netanyahu may no longer be alive. However, Israeli authorities have denied the claims and confirmed that the prime minister is alive and in good health.

The IRGC said Israeli attacks in different parts of the Middle East, particularly those that have resulted in civilian casualties, have further intensified tensions between the two countries.

The force added that if it is confirmed that Netanyahu is alive, it will continue to hunt him down until it takes what it described as appropriate action against him.

Tensions between Iran and Israel continue to escalate across the Middle East, raising concerns among the international community about the possibility of the conflict expanding into a wider regional war.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: