Aƙalla Mutane Shida ne suka mutu, a UAE Sakamakon harin da Iran ta Kai.

Aƙalla Mutane Shida ne suka mutu, a UAE Sakamakon harin da Iran ta Kai.

Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama, ciki har da ’yan Najeriya, suka jikkata sakamakon sabon harin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki da Iran ta kai kan ƙasar hadaddiyar daulan larabawa, UAE.

Rahotanni sun ce hare-haren sun faru ne a wasu muhimman wurare a ƙasar bayan makamai masu linzami da dama da jiragen drone suka fado a yankunan da ke da cunkoson jama’a.

Hukumomin tsaron UAE sun bayyana cewa tsarin kariyar sararin samaniyarsu ya yi nasarar tarwatsa wasu daga cikin makaman da aka harba, amma wasu sun kai ga faɗowa a wasu wurare lamarin da ya jawo asarar rayuka da jikkata mutane.

An tabbatar cewa daga cikin waɗanda suka jikkata akwai ’yan ƙasashe daban-daban da suka hada da Najeriya, yayin da jami’an lafiya suka ce yawancin waɗanda suka samu raunuka suna karɓar magani a asibitoci.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke kara tsananta tsakanin Iran da Israi'la da kuma Amurka tare da ci gaba da haifar da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Masana harkokin tsaro sun yi gargadin cewa ci gaba da irin waɗannan hare-hare na iya janyo faɗaɗar rikicin zuwa wasu ƙasashen yankin Gulf, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin ƙasashen duniya.

News Translation in English Language.

At Least Six Killed in Iran’s Attack on UAE.

At least six people have been confirmed dead while several others, including Nigerian nationals, were injured following a fresh wave of missile and drone attacks launched by Iran on the United Arab Emirates (UAE).

Reports indicate that the strikes targeted several key locations across the country, as multiple missiles and unmanned aerial vehicles crashed into densely populated areas.

UAE security authorities stated that their air defense systems successfully intercepted some of the incoming missiles. However, others managed to hit certain locations, resulting in casualties and injuries.

Officials confirmed that among those wounded are citizens of different countries, including Nigerians. Medical authorities added that most of the injured victims are currently receiving treatment in hospitals.

The attack comes amid escalating tensions involving Iran, Israel, and the United States, which continue to fuel instability across the Middle East.

Security analysts have warned that continued attacks of this nature could further expand the conflict to other Gulf countries, raising concerns among the international community.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: