Tsarin mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ba Zai Girgiza Ba don An kashe wani jagora - Abbas Araghchi.

Tsarin mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ba Zai Girgiza Ba don An kashe wani jagora - Abbas Araghchi.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya mayar da martani kan kisan manyan jami’an ƙasar, Ali Larijani da kuma kwamandan rundunar Basij, Gholamreza Soleimani, yana mai jaddada cewa tsarin Jamhuriyar Musulunci an gina shi ne ta yadda zai iya jure manyan rashe-rashen jagorori.

Araghchi ya bayyana cewa duk da asarar irin waɗannan manyan shugabanni, babu wani mutum guda da zai iya rushe ko raunana tsarin mulkin ƙasar. 
Ya ce tsarin Iran ya ta’allaka ne kan tsari mai ƙarfi da kuma akida, ba wai kan mutum ɗaya ba.

Wannan furuci na zuwa ne bayan rahotanni da ke cewa an kashe Larijani da Soleimani a hare-haren da suka shafi yaƙin da ke ƙara tsananta tsakanin Iran da Isra’ila tare da haɗin gwiwar Amurka. 

Ministan ya ƙara da cewa irin waɗannan hare-hare ba za su karya gwiwar Iran ba, yana mai nuni da cewa ƙasar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare manufofinta da martabarta a yankin.

News Translation in English Language.

Iran’s System Will Not Be Shaken by Assassination of Leaders – Abbas Araghchi.

Iran’s Foreign Minister, Abbas Araghchi, has reacted to the killing of top Iranian officials, Ali Larijani and Basij commander Gholamreza Soleimani, stressing that the Islamic Republic’s system is built to withstand the loss of key figures.

Araghchi stated that despite the deaths of such high-ranking leaders, no single individual can destabilize or weaken the country’s political structure. He emphasized that Iran’s system is founded on strong institutions and ideology, rather than reliance on any one person.

His remarks come amid reports that Larijani and Soleimani were killed in attacks linked to the escalating conflict involving Iran, Israel, and the United States.

The foreign minister further asserted that such attacks would not break Iran’s resolve, noting that the country will continue to stand firm in defending its policies and regional influence.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: