Babban lauya, Barista Abba Hikima, ya hadu da Malam Haruna Bashir—mutumin da aka yi wa iyalinsa kisan gilla a watannin baya a unguwar Charanchi da ke jihar Kano—a ƙasa mai tsarki, yayin da suke gudanar da ibadar Umrah.
Lauyan ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya wallafa cewa:
> “Na yi farin cikin haduwa da Malam Haruna Bashir yanzu a Makka. Allah ya kara masa kwanciyar hankali, Ameen.”
Rahotanni sun nuna cewa haduwar ta zo ne a wani lokaci da Malam Haruna ke ci gaba da kokarin farfadowa daga mummunan al’amarin da ya same shi, inda mutane da dama suka nuna tausayi tare da yi masa addu’ar samun sauki da kwanciyar hankali.
News Translation in English Language.
Senior Lawyer Abba Hikima Meets Malam Haruna Bashir in Mecca During Umrah.
A senior lawyer, Barrister Abba Hikima, has met with Malam Haruna Bashir—the man whose entire family was brutally killed months ago in Charanchi area of Kano State—in the holy city of Mecca during the Umrah pilgrimage.
The Lawyer disclosed this in a post on his Facebook page, where he wrote:
> “I am delighted to have met Malam Haruna Bashir in Mecca. May Allah grant him peace of mind, Ameen.”
Reports indicate that the meeting comes at a time when Malam Haruna is still recovering from the tragic incident, with many people expressing sympathy and offering prayers for his healing and comfort.

0 Comments:
Post a Comment