Babban Jami’in cibiyar dake yaƙi da ta’addanci na Amurka ya yi murabus saboda yaƙin Iran.

Babban Jami’in cibiyar dake yaƙi da ta’addanci na Amurka ya yi murabus saboda yaƙin Iran.

Babban jami’in cibiyar dake yaƙi da ta’addanci na Amurka ya yi murabus a yau Talata domin nuna adawa da yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran, inda ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta haifar da wata barazana kai tsaye ga Amurka.

A cikin wasiƙar murabus ɗinsa zuwa ga Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, daraktan Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Ƙasa, Joseph Kent, ya ce:

“Ba zan iya, cikin lamiri na, ci gaba da goyon bayan wannan yaƙi da ake yi a Iran ba.”

Kent ya ƙara da cewa Iran ba ta da wata barazana mai gaggawa ga tsaron ƙasar Amurka, lamarin da ya sa ya ɗauki matakin yin murabus daga mukaminsa.

News Translation in English Language.

US Counterterrorism Chief Resigns Over Iran War.

A senior official at the United States’ counterterrorism center has resigned on Tuesday in protest against the ongoing war involving the US and Israel against Iran, stating that the Islamic Republic of Iran poses no direct threat to the United States.

In his resignation letter addressed to US President Donald Trump, the Director of the National Counterterrorism Center, Joseph Kent, said:

“I cannot, in good conscience, continue to support the ongoing war in Iran.”

Kent further stated that Iran does not pose any immediate threat to US national security, a position that led him to step down from his role.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: