Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi gargadin cewa duk wata gaba ko rikici tsakanin ƙasashen Musulmi babu abun da zai haifar face ƙara ƙarfafa Israi'la, Inda yayi kira ga haɗin kai a tsakanin al’ummar Musulmi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, Pezeshkian ya jaddada cewa ƙasarsa ba ta da niyyar shiga rikici da makwabtanta ko sauran ƙasashen Musulmi, yana bayyana su a matsayin ‘yan’uwa. Ya ce rikice-rikicen cikin gida a tsakanin ƙasashen Musulmi na raunana yankin tare da buɗe ƙofa ga maƙiya su amfana.
Ya kuma ƙara da cewa dole ne ƙasashen Musulmi su fifita haɗin kai da fahimtar juna domin magance matsalolin yankin, maimakon rikici da sabani da ka iya janyo ƙaruwar rashin zaman lafiya.
Kalaman shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, inda rikice-rikice ke ci gaba da ƙara tsananta, lamarin da ke haifar da barazana ga tsaro da tattalin arzikin duniya.
Pezeshkian ya sake jaddada cewa Iran na da burin kyautata dangantaka da maƙwabtan ta, tare da gargadin cewa ci gaba da rarrabuwar kai tsakanin ƙasashen Musulmi zai ƙara tsawaita rikici da kuma ƙarfafa matsayin Israi'la a yankin.
News Translation in English Language.
Conflicts Among Muslim Nations Will Only Benefit Israel – Pezeshkian.
The President of Iran, Masoud Pezeshkian, has warned that conflicts and divisions among Muslim countries will yield no outcome other than strengthening Israel, calling for unity among the Muslim world.
In a statement issued on Saturday, Pezeshkian stressed that his country has no intention of engaging in conflict with its neighbors or other Muslim nations, describing them as brothers. He noted that internal disputes among Muslim countries weaken the region and create opportunities for adversaries to benefit.
He further emphasized that Muslim nations must prioritize unity and mutual understanding in addressing regional challenges, rather than engaging in conflicts and disagreements that could escalate instability.
The president’s remarks come at a time of rising tensions in the Middle East, where ongoing conflicts continue to intensify, posing threats to regional security and the global economy.
Pezeshkian reiterated that Iran is committed to maintaining good relations with its neighbors, warning that continued division among Muslim countries will prolong instability and further strengthen Israel’s position in the region.

0 Comments:
Post a Comment