Al’ummar Jihar Sokoto State sun fito da dumbin yawa domin tarbar Sarkin musulmi,Muhammadu Sa’ad Abubakar bayan dawowarsa gida bayan shafe kusan watanni uku ba ya cikin jihar.
Rahotanni sun nuna cewa jama’a sun cika tituna da wuraren taro domin nuna farin ciki da girmamawa ga Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne jagoran Musulmi a Nigeria. An bayyana yanayin tarbar da cike da murna da farin ciki, inda aka ga jama’a suna yi masa barka da zuwa.
Dawowar Sarkin Musulmi na zuwa ne a wani muhimmin lokaci na addini, inda jagorancinsa ke taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar al’ummar Musulmi kan al’amuran ibada da zamantakewa.
Masu lura da al’amura sun ce wannan tarba mai tarin jama’a na nuna irin ƙauna da haɗin kai da ke tsakanin Sarkin Musulmi da al’ummar Sakkwato, tare da ƙarfafa matsayinsa a matsayin ginshiƙi a harkokin addini da zamantakewa.

0 Comments:
Post a Comment