Matatar man fetur na Dangote ta sanar da ƙarin farashin man fetur zuwa N1,275 kan kowace lita, wanda ya zama karo na biyar da aka yi ƙarin farashin a cikin watan Maris na wannan shekarar, 2026.
Rahotanni sun nuna cewa sabon farashin ya tashi ne daga kusan N1,245 kan kowace lita, inda aka samu ƙarin kusan N30.
An ce wannan sabon tsari ya fara aiki ne a yau 21 ga Maris, 2026.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ganin sauye-sauyen farashin man fetur a ƙasar, lamarin da ke nuna yadda kasuwar man fetur ke fama da rashin daidaito a halin yanzu.
Dalilan Ƙarin Farashin.
Masana sun danganta wannan ƙarin da wasu muhimman dalilai, ciki har da:
Hauhawar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Matsin tattalin arziki da ya shafi canjin kuɗaɗen waje
Ci gaba da tsarin sassauta kasuwar man fetur a Najeriya
Tasirin Karin Ga ‘Yan Ƙasa
Ana sa ran wannan ƙarin farashi zai haifar da:
Ƙarin tsadar man fetur a gidajen mai
Tashin kuɗin sufuri da na kayan abinci.
Ƙarirn matsin rayuwa ga al’umma.
Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.
News Translation in English Language.
Dangote Refinery Raises Petrol Price to ₦1,275 Per Litre for Fifth Time in March.
The Dangote Petroleum Refinery has increased the price of Premium Motor Spirit (petrol) to ₦1,275 per litre, marking the fifth price adjustment within March 2026.
According to reports, the new price represents an increase from approximately ₦1,245 per litre, indicating a rise of about ₦30. The revised pricing is said to have taken effect on March 21, 2026.
The latest adjustment comes amid continued fluctuations in petrol prices across Nigeria, reflecting ongoing instability in the downstream petroleum market.
Factors Behind the Increase:
Industry analysts attribute the price hike to several factors, including rising global crude oil prices, persistent foreign exchange challenges, and the continued deregulation of Nigeria’s petroleum sector.
Implications for Nigerians:
The increase is expected to lead to higher pump prices nationwide, which may in turn drive up transportation costs and the prices of goods and services. This development is likely to further strain household incomes as citizens continue to face rising living costs.

0 Comments:
Post a Comment