Akwai hasashen rushewar Daular Isra’ila nan da shekarar 2027 - Sheikh Farfesa Mansur Isa Yelwa.

Akwai hasashen rushewar Daular Isra’ila nan da shekarar 2027 - Sheikh Farfesa Mansur Isa Yelwa.

Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Farfesa Mansur Isa Yelwa, ya bayyana cewa akwai hasashen rushewar Daular Isra’ila nan da shekarar 2027.

A cewarsa, tun a shekarar 1998 ne wani shahararren malami, Sheikh Ahmad Yasin, ya yi irin wannan hasashe cewa Daular Isra’ila za ta iya kawo ƙarshe zuwa wannan lokaci.

Farfesa Yelwa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da kafar Aljazeera, inda ya ce ya gudanar da bincike mai zurfi kan tarihin Banu Isra’ila. Ya ce a yawancin lokuta, daulolinsu kan ɗauki kimanin shekaru 40 kafin su rushe, sannan daga baya su sake farfaɗowa.

Ya kuma ƙara da cewa bayan fitar da wannan hasashe, an kashe Sheikh Ahmad Yasin bayan wasu shekaru, abin da ya ce ba zai rasa nasaba da irin wannan furuci ba.

Malamin ya bayyana wadannan bayanai ne a cikin wani faifan bidiyo na karatunsa da ke yawo a shafukan sada zumunta.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: