Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC na shirin gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban kotu a Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa gurfanarwar na daga cikin binciken da hukumar ke yi kan zarge-zargen aikata laifukan cin hanci da rashawa. Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan tuhume-tuhumen da ake yi masa ba.
Majiyoyi sun ce za a saurari karar a wata kotu da ke Kaduna, inda ake sa ran El-Rufai zai kare kansa daga zarge-zargen da hukumar ta ICPC ta gabatar.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da ICPC ke kara kaimi wajen yaki da cin hanci da rashawa, tare da mayar da hankali kan manyan jami’an gwamnati na yanzu da na baya, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin mulki a Najeriya.
News Translation in English Language.
ICPC Moves to Arraign El-Rufai Over Alleged Corruption in Kaduna.
The Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) has concluded plans to arraign former Kaduna State Governor, Nasir El-Rufai, before a court in Kaduna over alleged corruption-related offences.
According to reports, the planned arraignment follows ongoing investigations by the anti-graft agency into activities linked to El-Rufai during his time in office. While the exact nature of the charges has not been fully made public, officials say the case forms part of a broader effort to hold public office holders accountable.
Sources familiar with the matter disclosed that the proceedings are expected to commence in Kaduna, where the former governor will be required to enter his plea and respond to the allegations.
The development underscores the ICPC’s renewed push to strengthen its anti-corruption drive, as authorities continue to scrutinize the conduct of both serving and former government officials in Nigeria.
Observers say the case could become a significant test of the country’s commitment to transparency, rule of law, and institutional accountability.

0 Comments:
Post a Comment