An tsaurara matakan tsaro a harabar Kotun Tarayya da ke Kaduna a yau Talata, yayin da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, a gaban kotu.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro da dama dauke da makamai ne aka jibge a harabar kotun domin tabbatar da tsaro da kuma dakile duk wata barazana, sakamakon muhimmancin shari’ar da kuma hankalin jama’a da ta ja.
Ana tuhumar El-Rufai da laifuka da suka hada da zargin damfara da halasta kudaden haram, da kuma karkatar da kadarorin jama’a ba bisa ka’ida ba.
Kafin gurfanar da shi, an tsare shi na tsawon makonni, inda da farko Hukumar EFCC ta kama shi, kafin daga bisani ICPC ta sake kama shi tare da ci gaba da tsare shi har zuwa lokacin da aka gurfanar da shi a kotu.
Gurfanarwar na zuwa ne bayan matsin lamba daga ‘yan siyasa, iyalai da kungiyoyin fararen hula, wadanda suka bukaci a gurfanar da shi a gaban kotu ko kuma a sake shi idan babu hujjojin tuhuma.
Shari’ar na daga cikin manyan shari’o’in da ke daukar hankalin jama’a a Najeriya, musamman ganin cewa tana da alaka da tsohon gwamna da kuma manyan zarge-zargen cin hanci da rashawa.
News Translation in English Language.
Tight Security as ICPC Arraigns El-Rufai in Kaduna.
Security was significantly heightened at the Federal High Court in Kaduna on Tuesday as the Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) arraigned former Kaduna State Governor, Nasir Ahmad El-Rufai.
Reports indicate that heavily armed security personnel were deployed around the court परिसर to maintain order and prevent any potential security breach, given the high-profile nature of the case and the public attention it has attracted.
El-Rufai is facing multiple charges, including allegations of fraud, money laundering, and unlawful conversion of public assets.
Prior to his arraignment, he had reportedly been in detention for several weeks. He was initially arrested by the Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) before being re-arrested by the ICPC, which continued his detention until his court appearance.
The arraignment follows mounting pressure from political figures, family members, and civil society groups who had called on authorities to either formally charge him or release him.
The case is considered one of the most prominent ongoing corruption trials in Nigeria, involving a former state governor and serious financial crime allegations, thereby drawing widespread public and political interest.

0 Comments:
Post a Comment