Wata Matashiya 'yar Najeriya mai shekaru 23 da ke Amurka ta mutu a hatsarin mota.

Wata Matashiya 'yar Najeriya mai shekaru 23 da ke Amurka ta mutu a hatsarin mota.

Wata matashiya 'yar asalin Najeriya mai shekaru 23, wacce ta kammala karatun digiri kuma take zaune a ƙasar Amurka, ta rasu bayan da wata mota ta buge ta a wani hatsari, inda direban motar ya tsere daga wurin ba tare da tsayawa ba.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wani yanki na Amurka, inda aka ce motar ta bugi matashiyar sannan direban ya gudu, lamarin da ake kira hit-and-run.

Hukumomin tsaro sun fara bincike tare da ƙoƙarin gano direban da ya tsere domin gurfanar da shi a gaban doka. 
Har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan inda hatsarin ya faru da kuma yadda lamarin ya auku ba.

Wannan al’amari ya jawo alhini da jimami a tsakanin iyalan mamacin da al’ummar ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje.

News Translation in English Language.

23-Year-Old US-Based Nigerian Graduate Killed in Hit-and-Run Accident.

A 23-year-old Nigerian graduate based in the United States has died after being struck by a vehicle in a hit-and-run incident, with the driver fleeing the scene.

Reports indicate that the tragic incident occurred in a part of the US, where the victim was hit by a car. The driver reportedly escaped immediately after the crash without stopping.

Law enforcement authorities have launched an investigation and are working to identify and apprehend the fleeing driver. Further details regarding the exact location and circumstances surrounding the incident are yet to be disclosed.

The incident has sparked grief and mourning among the victim’s family, friends, and members of the Nigerian community in the diaspora.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: