An Naɗa Mohammad Baqer Zolqadr a Matsayin Sabon Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasar Iran.

An Naɗa Mohammad Baqer Zolqadr a Matsayin Sabon Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasar Iran.

Gwamnatin Iran ta sanar da naɗa Mohammad Baqer Zolqadr a matsayin sabon sakataren Majalisar Tsaron ƙasar, wanda ke kula da manyan harkokin tsaro da manufofin ƙasa.

Mohammad Baqer Zolqadr ya maye gurbin Marigayi Dr Ali Lirijani wanda ya rasu a harin da Israi'la da Amurka suka Kai makon da ya gabata.

Zolqadr, tsohon babban jami’i a rundunar IRGC kuma gogaggen masani a fannin tsaro, ya karɓi wannan muƙami ne a wani muhimmin lokaci da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tsaro da siyasa.

Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran na da muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin tsaro, harkokin waje da kuma yanke shawara kan manyan batutuwan da suka shafi tsaron ƙasa, inda take haɗa manyan jami’an gwamnati da na soji.

Ana kallon wannan naɗi a matsayin wani muhimmin mataki da zai iya tasiri a kan yadda Iran za ta tafiyar da harkokin tsaronta da hulɗarta da ƙasashen waje a wannan lokaci mai cike da ƙalubale.

News Translation in English Language.

Mohammad Baqer Zolqadr Appointed New Secretary of Iran’s Supreme National Security Council.

The Iranian government has appointed Mohammad Baqer Zolqadr as the new Secretary of the Supreme National Security Council, the body responsible for the country’s major security and policy decisions.

Zolqadr, a former senior officer in the Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) and an experienced security expert, assumes the role at a critical time as Iran faces significant security and political challenges.

The Supreme National Security Council plays a key role in shaping Iran’s security policies, foreign affairs, and major national security decisions, bringing together senior government and military officials.

This appointment is seen as a significant step that could influence how Iran manages its security and international relations during a period of heightened challenges.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: