Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa jihar Zamfara domin halartar taron karɓar gwamnan jihar, Dauda Lawal, zuwa jam’iyyar APC, bayan sauya sheƙarsa daga jam’iyyar PDP.
An shirya wannan gagarumin taro ne a birnin Gusau, inda ake sa ran halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC na ƙasa da na jiha, tare da dimbin magoya baya domin shaida wannan muhimmin sauyi na siyasa.
Sauya shekar Gwamna Lawal na zuwa ne a wani lokaci da ake ci gaba da ganin sauye-sauyen siyasa a faɗin ƙasar, yayin da jam’iyyun ke ƙoƙarin ƙarfafa matsayinsu gabanin zaɓukan gaba.
News Translation in English Language.
Shettima Arrives in Zamfara to Receive Governor Dauda Lawal into APC.
Vice President Kashim Shettima has arrived in Zamfara State to attend the official reception of Governor Dauda Lawal into the All Progressives Congress (APC), following his defection from the Peoples Democratic Party (PDP).
The grand event is scheduled to take place in Gusau, the state capital, and is expected to attract top APC leaders at both national and state levels, alongside a large crowd of supporters witnessing the significant political development.
Governor Lawal’s defection comes amid ongoing political realignments across the country, as parties continue to strengthen their positions ahead of future elections.

0 Comments:
Post a Comment