Wasu 'yan uwan juna mutum biyar sun rasa ransu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a Jihar Yobe ranar Laraba, 25 ga Maris, 2026.
An tabbatar da cewa mamatan sun hada da: Hajjagana Dahiru Zayi da Ibrahim Dahiru Zayi da Muhammad Dahiru Zayi da Hauwa Dahiru Zayi da wani ɗan uwan ahalin, wadanda duk mazauna Karamar Hukumar Potiskum ne.
Wani ɗan uwa ga mamatan, Dahiru Musa Talba ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani rubutu a shafinsa na Facebook, inda ya ce wasu ‘yan uwa guda uku sun ji rauni daban-daban.
Talba ya ce waɗanda suka ji rauni an garzaya da su zuwa Asibitin Gwamnati na Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, inda suke karɓar kulawar lafiya a halin yanzu.
Mai magana da yawun ‘yan sanda na Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa an tabbatar da mutuwar mutanen a hatsarin, yayin da wasu suka samu rauni.

0 Comments:
Post a Comment