Hambararren Shugaban ƙasar Venuzuela, Nicolas Maduro zai bayyana a gaban kotun Amurka.


Tsohon Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolás Maduro, zai bayyana a gaban wata kotun tarayya a birnin New York na ƙasar Amurka a yau Alhamis, 26 ga Maris, 2026, a wani shari’a mai matuƙar jan hankali a duniya. 
Wannan zama na kotu ya biyo bayan tuhumarsa da Amurka ta gabatar masa ne kan laifukan ta’addanci ta hanyar safarar miyagun ƙwayoyi da kuma manyan laifuka na shigo da kayan maye da makamai.

Ana tuhumar Maduro da matarsa, Cilia Flores, da laifuka da suka haɗa da ƙarawa da wasu ‘yan gwagwarmaya haɗin guiwa wajen safarar babban adadin ƙwayoyi da ƙoƙarin samar da makamai Zuwa cikin Amurka. 
Sai dai sun ƙaryata dukkan laifukan da ake tuhumarsu, inda suka bayyana cewa ba su da laifi.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: