Ƙasar Finland ta sake zama ƙasa wacce 'yan ƙasar suka fi rayuwa cikin farin ciki a duniya, inda ta zama ta farko a Rahoton na 2026 sannan ta ci gaba da mamaye jerin ƙasashe masu jin daɗin rayuwa a duniya.
An danganta ci gaba da samun wannan matsayi na Finland ga amintaccen zamantakewa da ingantaccen shugabanci, da ayyukan jama’a masu inganci, haka kuma da daidaiton aikin rayuwa da kusanci da yanayi.
Kamar yadda alkaluma Suka nuna a Rahotan na ranar Alhamis, daga rahoton shekara-shekara da ake samarwa tare da haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ke jera ƙasashe bisa yadda ‘yan ƙasa ke kimanta jin daɗin rayuwarsu.
Hakanan rahoton yana la’akari da muhimman alamomi kamar matakan samun kuɗi da tallafin zamantakewa da tsawon rayuwa da ‘yanci da alherin mutane da ra’ayin jama’a game da cin hanci da rashawa.
Sababbin ƙasashen sun fi rinjaye ne daga ƙasashen Turai, musamman waɗanda ke yankin da ake kira Nordic:
Ga jerin ƙasashen 10 da 'yan ƙasar suka fi samun farin ciki a shekarar 2026.
Finland
Denmark
Iceland
Sweden
Netherlands
Costa Rica
Norway
Israel
Luxembourg
Mexico.

0 Comments:
Post a Comment