Atiku Ya Bukaci A Saki Ko A Gurfanar da Sheikh Sani Khalifa Zaria Kai Tsaye.

Atiku Ya Bukaci A Saki Ko A Gurfanar da Sheikh Sani Khalifa Zaria Kai Tsaye.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su saki Sheikh Sani Khalifa Zaria nan take ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu ba tare da wani jinkiri ba, saboda yadda ake ci gaba da tsare shi ba tare da izinin kotu ba — abin da Atiku ya bayyana a matsayin keta hakkin ɗan Adam da kuma mummunar karya tsarin kundin mulkin ƙasa. 

Atiku ya ce Sheikh Khalifa, malamin addini daga Jihar Kaduna, Wanda akae tsare da shi tun a watan Disamba 2025, bisa zarge‑zargen da ake masa na hannu a wani shirin juyin mulki amma ba a mika masa tuhumar a kotu ba. 

Ya bayyana cewa ci gaba da tsare shi lokaci mai tsawo ba tare da gabatarwa a kotu ba yana haifar da babban abin damuwa ga tsarin mulki da hakkin ɗan Adam a ƙasar, kuma ya yi kira ga cewa ba wata hukuma da ta fi ƙarfin Kundin Tsarin Mulki. 

Atiku ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da tsare Sheikh Khalifa ba tare da izinin ganin iyalinsa da lauyoyinsa da kuma kulawar lafiyarsa ba — abin da ya ce hakan keta doka da haƙƙoƙin ɗan ƙasa ne. 

Ya kuma yi gargadi cewa irin wannan dabi’a na tsarewa ba tare da gurfanarwa a gaban kotu ba zai iya raunana tushe da ‘yancin dimokuraɗiyya a Najeriya, kuma ya bukaci a yi biyayya da umarnin kotu don tabbatar da adalci. 

News Translation in English Language.

Atiku Calls for Immediate Release or Trial of Sheikh Sani Khalifa Zaria.

Former Vice President Atiku Abubakar has called on security authorities to either immediately release Sheikh Sani Khalifa Zaria or bring him to court without further delay, citing concerns over his continued detention without court authorization — an act Atiku described as a violation of human rights and a serious breach of the nation’s constitution.

Atiku noted that Sheikh Khalifa, a religious scholar from Kaduna State, has been in detention since December 2025 over alleged involvement in a purported coup plot, yet no formal charges have been filed against him in court.

He stated that prolonged detention without court presentation raises serious concerns about the rule of law and human rights in the country, emphasizing that no authority is above the Constitution.

Atiku also expressed concern over Sheikh Khalifa being held without access to his family, lawyers, or adequate medical care, calling such treatment a breach of the law and citizens’ rights.

He further warned that detention without trial could undermine the foundations of democracy in Nigeria and urged authorities to comply with court orders to ensure justice is served.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: