Iran ta yi watsi da bukatar Amurka da ta gabatar domin kawo ƙarshen rikicin da ke gudana a tsakaninsu, tana mai jaddada cewa za ta amince da tsagaita bude wuta ne kawai idan an cika sharuɗɗanta.
Wata majiya mai tushe daga gwamnatin Iran ta bayyana cewa Iran ba ta yarda da shirin da Amurka ta gabatar ba, tana mai cewa shirin bai dace da bukatun ƙasar ba.
Ta kuma ƙara da cewa Iran ce za ta yanke lokacin da yaƙin zai ƙare, bisa ga muradunta da sharuddan da ta gindaya.
Sharuɗɗan da Iran Ta Gindaya:
Rahotanni sun nuna cewa Iran ta shimfiɗa manyan sharuɗɗa guda biyar kamar haka:
1. Dakatar da dukkan hare-haren Amurka da Isra’ila, ciki har da kisan gilla
2. Bayar da tabbacin tsaro mai ƙarfi domin hana sake kai hare-hare a nan gaba
3. Biya diyya kan asarar da aka yi sakamakon yaƙin
4. Dakatar da faɗa a dukkan fannoni, har da waɗanda ke da alaƙa da Iran a yankin
5. Amincewa da ikon Iran a mashigar ruwan Hormuz
Wannan mataki na Iran na nuna tsauraran matakai, wanda ke ƙara dagula yiwuwar cimma yarjejeniyar sulhu cikin gaggawa. Iran na neman tabbacin tsaro, diyya, da kuma amincewa da wasu muhimman muradunta kafin ta amince da kawo ƙarshen rikicin.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta gabatar da wani shiri mai kunshe da maki 15 ta hannun masu shiga tsakani. Sai dai Iran ta nuna rashin yarda da irin waɗannan shawarwari, tana mai zargin cewa a baya an yi irin hakan amma daga bisani aka kai hare-hare.
Rikicin dai na ci gaba da ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ke haifar da fargaba a duniya, musamman dangane da tsaron hanyoyin jigilar mai.
News Translation in English Language.
Iran Sets Five Conditions to End War with Israel and the United States.
Iran has rejected a proposal put forward by the United States aimed at ending the ongoing conflict, insisting it will only agree to a ceasefire if its conditions are fully met.
A senior source within the Iranian government stated that Tehran does not accept the U.S. plan, describing it as inconsistent with the country’s interests. The source added that Iran alone will determine when the war comes to an end, based on its own objectives and outlined conditions.
Reports indicate that Iran has presented five key demands:
1. A complete halt to all U.S. and Israeli attacks, including targeted killings
2. Firm security guarantees to prevent future military actions
3. Compensation for damages and losses caused by the war
4. An end to fighting across all fronts, including groups aligned with Iran in the region
5. Recognition of Iran’s authority over the Strait of Hormuz
Iran’s stance reflects a hardline position that may further complicate efforts to reach a swift peace agreement. The country is demanding security assurances, reparations, and recognition of its strategic interests before agreeing to end the conflict.
Reports suggest that the United States had proposed a 15-point plan through mediators. However, Iran has expressed distrust toward such proposals, alleging that similar efforts in the past were followed by renewed attacks.
The conflict continues to escalate across the Middle East, raising global concerns, particularly over the security of vital oil shipping routes.

0 Comments:
Post a Comment