'Yan bindiga sun kashe sojoji da dama tare da wani jami’in dan sanda a wani mummunan harin kwanton bauna da suka kai a Jihar Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a kauyen Giron Masa da ke karamar hukumar Shanga, inda jami’an tsaro suka je bayan samun bayanan sirri daga mazauna yankin kan motsin wasu ‘yan bindiga.
Majiyoyi sun ce jami’an tsaron sun fuskanci harin ne kafin su isa inda ake zargin ‘yan bindigar suke, inda aka yi musu kwanton bauna mai tsanani.
Akalla sojoji 9 da dan sanda 1 ne suka rasa rayukansu a harin.
Haka kuma, an ruwaito cewa wani farar hula ya mutu yayin da wasu da dama suka jikkata.
‘Yan bindigar sun kuma kona motocin sojoji, ciki har da manyan motocin yaki, lamarin da ya kara dagula al’amura a yankin.
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi Allah wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici.
Ya kuma ziyarci wadanda suka jikkata a asibiti tare da alkawarin tallafawa iyalan wadanda suka rasu.
Ko da yake babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, ana zargin cewa ‘yan bindiga ko kungiyoyin ‘yan ta’adda ne ke da hannu, musamman wadanda ke aiki a yankunan Arewa maso Yamma.
Wannan hari na daga cikin jerin hare-haren da ke nuna kara tsananta matsalar tsaro a Arewacin Najeriya, inda ake yawan kai hare-hare kan jami’an tsaro da fararen hula.
News Translation in English Language.
Gunmen Kill Soldiers and Policeman in a Deadly Ambush in Kebbi Stare.
Armed gunmen carried out a deadly ambush that killed several soldiers and a police officer in Kebbi State, highlighting the worsening security situation in the region.
The attack occurred in Giron Masa village, Shanga Local Government Area, where security forces had been deployed following credible intelligence from local residents about suspicious armed men in the area.
Before reaching their target, the troops were caught in a sudden and violent ambush by the gunmen.
Reports confirm that at least 9 soldiers and 1 police officer lost their lives.
Additionally, a civilian was reportedly killed, while several others sustained various injuries.
The attackers also destroyed and set fire to military vehicles, including tactical trucks, worsening the situation on the ground.
Kebbi State Governor, Nasir Idris, condemned the attack, describing it as tragic.
He visited the injured in the hospital and promised support for the families of the deceased and the wounded.
No group has officially claimed responsibility, but local authorities suspect armed bandit groups operating in northwestern Nigeria.
Experts say this attack demonstrates the increasing strength and tactics of armed groups, particularly in carrying out ambushes against security personnel in northern Nigeria.

0 Comments:
Post a Comment