Wata mata ta haifi ‘ya'ya biyar a jihar Kano.

Wata mata ta haifi ‘ya'ya biyar a jihar Kano

Rahotanni sun bayyana cewa an haifi jariran ne a asibitin kwararru na Murtala dake Kano, inda suka kunshi maza uku da mata biyu, kuma an haife su cikin koshin lafiya. Mijin matar, Malam Salisu Nafiu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa iyalin nasa na cikin farin ciki da godiya ga Allah bisa wannan ni’ima.

An ce haihuwar ‘yan biyar tana bukatar kulawa ta musamman daga likitoci, saboda irin hadarin da ke tattare da haihuwar yawan jarirai a lokaci guda.
An baiyana sunan matan da Hafsat Yusuf wacce Kafin Wannan haihuwar take da 'ya'ya takwas.

Wannan lamari ya ja hankalin al’umma, inda mutane da dama ke taya iyalin murna tare da addu’ar Allah Ya raya jariran cikin koshin lafiya.

News Translation in English Language.

Mother of Eight Gives Birth to Quintuplets in Kano.

A woman named Hafsatu Yusuf, who already has eight children, has given birth to quintuplets in Kano State.

Reports indicate that the babies—three boys and two girls—were delivered safely at a local hospital. Her husband, Malam Salisu Nafiu, confirmed the birth, expressing the family’s joy and gratitude to God for this remarkable blessing.

Medical experts note that the care of quintuplets requires special attention due to the complexities associated with multiple births.

The news has drawn widespread public interest, with many offering congratulations and prayers for the newborns’ health and well-being.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: