Rundunar sojin Israi'la ta sanar da mutuwar sojojinta huɗu a kudancin Lebanon.

Rundunar sojin Israi'la ta sanar da mutuwar sojojinta huɗu a kudancin Lebanon.

Rundunar Sojin Isra’ila ta sanar cewa sojojinta huɗu sun mutu a fagen daga a kudancin Lebanon, inda dakarun ƙasar ke fafatawa da mayakan Hezbollah bayan ƙaddamar da mamayar ƙasa a cikin ƙasar.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Talata, ta bayyana sunayen sojoji uku daga bataliya guda da suka “faɗi a yayin artabu”. A wata sanarwa ta daban kuma, rundunar ta ce wani soja ya mutu a wannan hari ɗaya, yayin da wasu biyu suka jikkata, ba tare da bayyana sunayensu ba.

An ruwaito cewa sojojin Isra’ila goma ne suka mutu tun bayan da rikici tsakanin Isra’ila da Hezbollah ya ɓarke a ranar 2 ga Maris, bayan harin haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila akan ƙasar Iran.

Fiye da mutane 1,200 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a kudancin Lebanon, a cewar Ma’aikatar Lafiyar ƙasar ta Lebanon, yayin da sama da mutane miliyan ɗaya suka rasa muhallansu.

News Translation in English Language.

The Israeli military has announced the deaths of four of its soldiers in southern Lebanon.

The Israeli army stated that four of its soldiers were killed in combat in southern Lebanon, where its forces are clashing with Hezbollah fighters following a ground invasion of the country.

In a statement released on Tuesday, the army named three soldiers from the same battalion who “fell during combat.” In a separate statement, it said another soldier was killed in the same incident, while two others were wounded, without disclosing their names.

It has been reported that ten Israeli soldiers have died since the conflict between Israel and Hezbollah erupted on March 2, following a joint U.S.-Israeli strike on Iran.

More than 1,200 people have been killed in Israeli attacks in southern Lebanon, according to the Lebanese Ministry of Public Health, while over one million people have been displaced.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: