Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-rufai Ya Rasa Mahaifiyarsa.

Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-rufai Ya Rasa Mahaifiyarsa.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya rasa mahaifiyarsa, Hajiya Safiya Ali Rufai, bayan gajeriyar rashin lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa marigayiyar ta rasu ne a ranar Sallah, lamarin da ya jefa iyali da al’ummar jihar Kaduna cikin jimami. 

A cikin sakonnin ta’aziyya da aka rika aikawa, an bayyana marigayiyar a matsayin mace mai tsoron Allah, mai tausayi da kuma uwa ga jama’a da dama.

Haka kuma, an yi kira ga al’umma da su taya iyalan addu’a domin Allah ya jikanta da rahama, ya kuma gafarta mata kurakuranta.

News Translation in English Language.

FORMER KADUNA GOVERNOR NASIR EL-RUFAI LOSES MOTHER.

Former Kaduna State Governor, Malam Nasir El-Rufai, has lost his mother, Hajiya Safiya Ali Rufai, after a brief illness.

Reports indicate that she passed away on the day of Eid, a development that has thrown her family and the people of Kaduna State into mourning.

In condolence messages that followed, the late matriarch was described as a God-fearing woman, compassionate, and a mother figure to many.

The public has also been urged to pray for her soul, asking God to grant her mercy and forgive her shortcomings.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: