Gwamnatin Jihar Filato ta kakaba dokar hana fita na tsawon awanni 48 a birnin Jos bayan harin da 'yan bindiga suka Kai.

Gwamnatin Jihar Filato ta kakaba dokar hana fita na tsawon awanni 48 a birnin Jos bayan harin da 'yan bindiga suka Kai.

Gwamnatin Jihar Filato ta sanar da kakaba dokar hana fita na tsawon awanni 48 a karamar hukumar Jos ta arewa bayan wani mummunan harin ‘yan bindiga da ya faru a Angwan Rukuba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 14 tare da raunata wasu. 

An fara aiwatar da dokar hana fitan ne daga tsakar daren ranar 29 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu, 2026, kuma an fitar da wannan sanarwa ne ta bakin kwamishinan masana’antu da sadarwar jihar, Rt. Hon. Joyce Lohya Ramnap. 

Gwamna Caleb Mutfwang ya yi Allah wadai da harin, inda ya bayyana shi a matsayin Abun takaicin da ba a yi zato ba kuma ba a haifar da wani dalili ba, sannan ya tabbatar wa al’umma cewa hukumomin tsaro sun tashi tsaye domin dawo da zaman lafiya da kuma kamo masu laifi. 

An bukaci mazauna yankin da su zauna lafiya, su bi dokar hana fita kuma su bai wa jami’an tsaro hadin kai domin taimakawa wajen bincike da tabbatar da doka ta yi aikinta. 

News Translation in English Language.

Plateau Government Imposes 48-Hour Curfew in Jos North Following Deadly Gun Attack.

The Plateau State Government has announced a 48-hour curfew in Jos North Local Government Area after a deadly attack by gunmen in the Gari Ya Waye, Angwan Rukuba community, which left several people dead and others injured.

The curfew is effective from midnight on March 29 until April 1, 2026, according to the state Commissioner for Industry and Communication, Rt. Hon. Joyce Lohya Ramnap.

Governor Caleb Mutfwang condemned the attack, describing it as senseless and unjustifiable, and assured residents that security agencies have been mobilized to restore peace and apprehend those responsible.

Residents have been urged to remain calm, comply with the curfew, and cooperate with security forces to aid ongoing investigations and ensure that justice is served.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: