Gwamna Zulum ya rusa Majalisar Zartarwar Jihar Borno.


Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rushe Majalisar Zartarwar Jihar, wanda hakan ya kawo ƙarshen aikin dukkan kwamishinoni da sauran masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin jihar.

A cewar sanarwar, wannan mataki ya fara aiki nan take, inda aka umarci dukkan kwamishinonin da abin ya shafa da su miƙa ragamar aiki ga manyan sakatarorin ma’aikatunsu domin ci gaba da tafiyar da ayyukan gwamnati ba tare da tangarda ba.

Wannan mataki na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na sake fasalin gwamnati, wanda ake sa ran zai ba da dama ga nada sababbin kwamishinoni ko sake naɗa wasu daga cikin tsofaffin domin inganta gudanarwa da ayyukan gwamnati.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa irin wannan mataki ba sabon abu ba ne a tsarin mulkin Najeriya, inda gwamnoni ke ɗaukar irin wannan mataki domin sabunta tsarin mulki da ƙara inganci a aiki, da kuma daidaita alkiblar tafiyar da gwamnati.

Ana sa ran nan gaba kaɗan Gwamna Zulum zai sanar da sabbin naɗe-naɗe domin cike guraben da aka bari.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: