Aƙalla Mutan 11 ne suka mutu yayin da gidaje sama da 50 suka ƙone a rikicin kabilanci a Nasarawa.


Akalla mutane goma sha ɗaya ne suka rasa rayukansu yayin da sama da gidaje 50 suka ƙone sakamakon rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a wasu ƙauyuka a Jihar Nasarawa. 

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya faru ne a tsakanin al’ummomin Akyawa da Udege Kasa, inda rikicin ya rikide zuwa tashin hankali mai tsanani, wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa. 

Harin ya tilasta wa mazauna yankunan tserewa daga gidajensu domin tsira da rayukansu, yayin da jami’an tsaro suka fara ɗaukar matakai domin dawo da zaman lafiya a yankin. 

Har yanzu hukumomi na ci gaba da bincike kan musabbabin rikicin tare da ƙoƙarin kamo waɗanda ke da hannu a wannan tashin hankali.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: