Yadda Iraniyawa Suka yi gangami a fadin Ƙasar Iran don girmama marigayi shugaban Addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.

Yadda Iraniyawa Suka yi gangami a fadin Ƙasar Iran don girmama marigayi shugaban Addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.

Dubban mutane ne a kasar Iran suka fito kan tituna domin karrama marigayi Jagoran Addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya rasu bayan harin da Amurka da Isra’ila suka kai a farkon rikicin da ya farke a karshen watan Fabrairu. 

An gudanar da gangamin ne a manyan birane da dama ciki har da Tehran da Urmia da Gorgan, inda mahalarta suka rika Ɗaga hotunan marigayin shugaban Addinin ƙasar suna nuna alhini da girmamawa gare shi. 

Rahotanni sun nuna cewa an fara wadannan taruka ne da safe a daidai lokacin da aka kashe Khamenei a ranar 28 ga watan Fabrairu, lamarin da ya tayar da rikicin da ya bazu a yankin gabas ta tsakiya. 

Duk da wadannan gangami, har yanzu ba a gudanar da jana’izar kasa baki daya ba sakamakon yakin da ke gudana. 

Marigayi Ali Khamenei ya shafe kusan shekaru arba’in yana jagorantar Iran kafin rasuwarsa, kuma dansa Mojtaba Khamenei ne ya gaje shi a matsayin sabon jagora.

0 $type={blogger}: