‘Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Na Soja Da Sojoji 17 A Borno.

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Na Soja Da Sojoji 17 A Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan ta’adda sun kai mummunan hari a jihar Borno, inda suka kashe wani babban jami’in soja mai mukamin Brigadier General tare da wasu sojoji 17.

Lamarin ya faru ne a wani sansanin soja da ke yankin Benisheikh, inda maharan suka kutsa cikin sansanin da sanyin safiya suka fara musayar wuta da dakarun tsaro.

Majiyoyi sun ce harin ya yi sanadin asarar rayuka da dama, ciki har da babban jami’in sojan, yayin da wasu sojoji suka jikkata a yayin artabun.

Rahotanni sun kuma nuna cewa maharan sun lalata wasu kayan aikin soja tare da kona motoci kafin su tsere daga wurin.

Hukumomin soji sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce an tura dakarun ƙarin ƙarfi domin bin sawun maharan tare da dawo da zaman lafiya a yankin.

Jihar Borno na ci gaba da fuskantar matsalolin hare-haren ‘yan ta’adda, musamman daga ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

0 $type={blogger}: