ƙasar Iran ta ba duniya mamaki a lokacin yaƙin ta da Amurka da Isra’ila - Mojtaba Khamenei.

ƙasar Iran ta ba duniya mamaki a lokacin yaƙin ta da Amurka da Isra’ila - Mojtaba Khamenei.

Jagoran Juyin juya halin Musuluncin ƙasar Iran Ayatollah Mojtaba Khamenei ya bayyana cewa ƙasar da kuma al’ummarta sun ba duniya mamaki a lokacin yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar akan kasar.

A cikin wani jawabi, Khamenei ya ce juriya da hadin kan da ‘yan ƙasar Iran suka nuna ya karya hasashen makiya, wadanda suka yi zaton za su iya raunana kasar cikin kankanin lokaci. Ya jaddada cewa hare-haren da aka kai ba su cimma manyan manufofinsu ba, yana mai cewa Iran ta tsaya tsayin daka duk da matsin lamba. 

Khamenei ya kara da cewa matakan da Iran ta dauka a lokacin yakin sun nuna karfin ƙasar da kuma iya kare kanta, lamarin da ya sa duniya ta yi mamaki da yadda kasar ta jure.

Ya kuma nanata cewa Iran ba za ta mika wuya ga matsin lambar kasashen waje ba, yana mai gargadin cewa duk wani sabon hari zai fuskanci martani mai tsauri daga Tehran. 

Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan sakamakon yakin, inda bangarorin biyu ke ikirarin samun nasara duk da barnar da aka samu.

0 $type={blogger}: