An ruwaito cewa Matashiyar 'yar shekara 14, ta gamu da ajalinta ne a lokacin da wani soja ya harba bindiga a wajen bikin abokin aikinsu a Unguwar ma’aikatan Jami’ar Asibitin Koyarwa na Maiduguri (UMTH), Lamarin da yasa arsashin ya same ta a cikin gidansu, Inda ta mutu nan take.
Yarinyar, wadda take dalibar makarantar sakandare, ta rasu nan take bayan harbin da ta samu, sannan aka yi Jana'izar ta a daren ranar Asabar.
Kungiyar Amnesty International ta bayyana bakin cikinta kan wannan lamari, inda ta yi kira ga hukumomin Najeriya su gudanar da cikakken bincike mai adalci kan yadda sojoji ke amfani da makamai a wuraren jama’a.
Haka zalika Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun jaddada cewa irin wannan rasuwa za a iya hana ta idan aka bi ka’idojin tsaro, tare da bukatar hukunci ga masu laifi.
Har zuwa yanzu, babu wani jawabi na hukuma daga rundunar sojojin Najeriya da aka fitar game da wannan lamari ko yadda ake gudanar da bincike a kansa.

0 Comments:
Post a Comment