Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa mutanen jihar Kano za su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya wajen sake tsayawa takara a zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan siyasar gaba da kuma makomar shugabancin ƙasar. Ya jaddada cewa al’ummar Kano na da niyyar ci gaba da ba da goyon baya ga shugabancin Tinubu, musamman idan aka ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su amfani jama’a.
Ya kuma ƙara da cewa hadin kai da ci gaban kasa na daga cikin manyan abubuwan da ke sa ake buƙatar ci gaba da goyon bayan shugabanci mai dorewa.
Kalaman gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan siyasar 2027 a sassa daban-daban na ƙasar.

0 Comments:
Post a Comment