Yadda wata mace mai fama da tabin hankali ta haifi jariri a gefen hanya a Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Kwaita da ke ƙaramar hukumar Kwali, da safiyar ranar 3 ga Afrilu, 2026. Rahotanni sun nuna cewa jami’an ‘yan sanda da ke sintiri sun samu labarin abin da ya faru, inda suka garzaya zuwa wurin domin kai dauki.
Da isarsu, sun tarar da matar tare da jaririnta da ta haifa a wajen. Nan take suka ceto su, tare da kai su asibiti mafi kusa domin samun kulawar likitoci.
An tabbatar da cewa duka uwa da jaririn suna cikin koshin lafiya bayan an basu kulawar da ta dace.
Bayan haka, hukumomi sun mika su ga sashen jin kai da walwalar jama’a, inda aka kai su cibiyar kula da masu bukata ta gwamnati domin samun cikakkiyar kulawa da kariya.
‘Yan sanda sun yaba da kokarin jami’an da suka shiga aikin ceton, tare da kira ga al’umma da su rika nuna tausayi da kuma sanar da hukumomi idan suka ga irin wadannan mutane masu bukatar taimako.

0 Comments:
Post a Comment