Wani Matashin dan Najeriya mai shekara 27 ya rasa ransa bayan rugujewar gini a ƙasar Cyprus.

Wani Matashin dan Najeriya mai shekara 27 ya rasa ransa bayan rugujewar gini a ƙasar Cyprus.

Wani matashin dan Najeriya mai suna Stanley, mai shekaru 27, ya rasu bayan wani bangare na ginin bene mai hawa hudu ya rufta a birnin Limassol da ke kasar Cyprus.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na rana a ranar Asabar ta Easter, 11 ga Afrilu, 2026, a titin Aeschylou da ke yankin Germasogeia, jim kadan bayan Stanley ya dawo gida daga tseren safe.

Rahotanni sun bayyana cewa ginin yana dauke da mazauna daga kasashen Afirka da Masar, inda wasu daga cikin mutane suka yi nasarar tserewa yayin da wasu kuma ba sa cikin gidan lokacin da rushewar ta faru.

Shaidu sun ce ginin yana da dakuna guda takwas zuwa tara, kuma a kowane daki akwai mutane kusan hudu, lamarin da ya tayar da hankali game da adadin mutanen da ka iya kasancewa a ciki lokacin hadarin.

Mazauna yankin sun ce sun ji wani babban kara, amma da farko sun dauka karar fashewar wutar bikin Easter ne da ake yi a lokacin bukukuwan tashin Yesu.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa an riga an ce ginin ba ya cikin yanayi mai kyau na zama.

Lamarin ya jawo gaggawar aikin ceto daga hukumar kashe gobara da ‘yan sanda, rundunar EMAK da jami’an kare fararen hula.

An gano gawar farko da misalin karfe 5:30 na yamma, sannan aka gano wata gawar bayan wasu sa’o’i.

An kai mutum uku da suka jikkata asibiti, kuma yanzu suna cikin kwanciyar hankali.

Ginin dai yana dauke da galibin mazauna kasashen waje, kuma an yi kiyasin cewa mutane kusan 20 ne ke zaune a cikin dakuna 10 zuwa 11 na ginin.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: