Rahotanni daga Pakistan sun bayyana cewa manyan jami’an Iran da na Amurka sun fara tattaunawa a babban birnin ƙasar, Islamabad, domin neman hanyar kawo ƙarshen yaƙin da ya shafe kusan makonni shida ana yi a tsakanin ƙasashen biyu a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan shi ne matakin farko na tattaunawa kai tsaye tsakanin ƙasashen biyu cikin shekaru da dama, kuma Pakistan ce ke jagorantar shiga tsakani domin taimakawa wajen cimma zaman lafiya a yankin.
Jami’an da ke halartar tattaunawar sun haɗa da wakilan gwamnatin Iran da na Amurka, inda ake tattaunawa kan muhimman batutuwa kamar tsagaita bude wuta da matsalolin takunkumi da kuma tsaron hanyoyin jigilar mai a yankin.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa akwai sabani mai ƙarfi tsakanin ɓangarorin biyu, duk da cewa an fara tattaunawar da fatan samun mafita ta dindindin ga rikicin.
Pakistan ta bayyana cewa tana fatan wannan shiri zai zama mataki mai muhimmanci wajen dawo da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

0 Comments:
Post a Comment