Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin karɓar sabon bashin kuɗi har dala miliyan 516.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Majalisar, Shugaban ƙasar ya bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa, musamman a ɓangarorin tattalin arziki da more rayuwa.
Tinubu ya jaddada cewa wannan bashi na daga cikin tsare-tsaren gwamnati na inganta ababen more rayuwa, ƙarfafa tattalin arziki, da kuma samar da ayyukan yi ga al’umma.
Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tattauna buƙatar tare da duba muhimmancinsa ga ci gaban ƙasa kafin yanke hukunci kan amincewa da shi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke ci gaba da neman hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da rage matsin tattalin arziki da ake fuskanta.

0 $type={blogger}:
Post a Comment