Rundunar ’Yan Sanda ta dakile harin ’yan bindiga a Sakkwato, ta kwato ƙwanson harsasai 167.

Rundunar ’Yan Sanda ta dakile harin ’yan bindiga a Sakkwato, ta kwato ƙwanson harsasai 167.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ta bayyana cewa ta yi nasarar dakile wani shiri na kai hari da wasu ‘yan bindiga suka yi a wasu yankunan jihar, tare da haɗin gwiwar sojoji da ‘yan sa-kai.

A yayin artabun, jami’an tsaron sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu guduwa daga wurin.

Bayan bin sawun su, jami’an sun gano ƙwanson harsasai 167 na bindiga da ‘yan bindigar suka bari a baya, waɗanda aka kwato a matsayin hujja.

Haka kuma, an gudanar da ƙarin samame a wasu yankuna inda aka kama wasu da ake zargi tare da kwato makamai da wasu kayayyaki da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan ta’addanci.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa waɗannan matakan na cikin ƙoƙarin da ake yi na karya lagon ‘yan bindiga da kuma inganta tsaro a jihar Sakkwato.

0 $type={blogger}: