Tinubu Ya Fara Shirin Tsayawa Takarar 2027, Inda aka Karɓi Fom din takara a Madadinsa.

Tinubu Ya Fara Shirin Tsayawa Takarar 2027, Inda aka Karɓi Fom din takara a Madadinsa.


Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya fara ɗaukar matakin tsayawa takarar shugaban ƙasa karo na biyu a babban zaɓen shekarar 2027, bayan da aka karɓi fom ɗin tsayawa takara a madadinsa.

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ikeja, James Faleke, ne ya karɓi fom ɗin a madadin shugaban, yayin wani taro da aka gudanar a Abuja.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin sakataren jam’iyyar APC, Suleiman Argungu, wanda ya ƙaddamar da fara sayar da fom ɗin ga masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Wannan mataki na nuni da fara shirye-shiryen siyasa a cikin jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027, yayin da ake sa ran masu neman takara za su fara bayyana ra’ayoyinsu a hukumance.

0 $type={blogger}: