Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya amince da shirin biyan Naira tiriliyan 3.3 don warware tsofaffin basussuka a sashen wutar lantarki na Najeriya, a karkashin Shirin Gyaran Harkar Kudi na Sashen Wutar Lantarki.
An dai bayyana cewa wadannan basussuka sun taru ne cikin fiye da shekaru goma tun daga (Feb 2015 – Maris 2025) kuma sun jawo matsaloli wajen samar da wuta mai dorewa a kasar.
Bayan bincike, gwamnatin ta amince cewa N3.3trn ce cikakkiyar adadin kudin da za a biya don kammala Shirin inganta wutar.
An fara aiwatar da shirin ne, inda tashoshin samar da wuta 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar biyan basussuka har N2.3trn. An tattara kimanin N501bn domin tallafawa shirin, ciki har da N223bn da aka riga aka raba.
Ana sa ran biyan wadannan basussuka zai karfafa kudi a duk sashen samar da wuta, wanda zai baiwa kamfanonin samar da wuta damar karbar kudinsu, gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, sannan hakan zai inganta samar da wuta. Hakanan, shirin yana daga cikin gyaran harkokin lantarki da suka hada da inganta tsarin metering da farashin wuta bisa yadda ake samu.
Sashen wutar lantarki a Najeriya ya sha fama da katsewar wuta, rashin biyan kamfanonin samar da wuta da masu isar da iskar gas, da matsalolin kudi. Wannan shirin biyan basussuka na daya daga cikin manyan matakan gyara da gwamnati ke dauka don kawar da wannan cikas.
Kwararru sun jaddada cewa biyan basussuka ba zai kawo sauyi nan take ba – ingancin samar da wuta zai dogara ne akan ci gaba da aiwatar da shirin da kuma ingancin kayan aikin samar da wuta. Har yanzu, yan Najeriya na fuskantar rashin wuta mai dorewa a ƙasar.
_9.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment