Jami’an ‘yan sandan jihar Kaduna sun bayyana cewa fashewar da aka ji a tashar Mando a daren Lahadi ba fashewar bam ba ce, karamin fashewar gas ne daga wata babbar mota mai amfani da Gas, inda aka bayyana cewa tankin gas din ya cika sosai ne kafin ya fashe.
A jawabin da jami’an suka fitar, lamarin wanda ya faru da misalin karfe 3 na safiyar Lahadi bai yi sanadiyyar mutuwar kowa ko raunana wani ba duk da hayakin fashewar da kara mai karfi da aka ji a wurin.
An ce motar ta kasance daga kamfanin Silver Luxury Travel kuma tana jiran fara jigilar fasinjoji ne, kafin fashewar ta afku.
‘Yan sandan sun yi gargadi ga jama’a da kafofin watsa labarai su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yada su, domin gujewa jawo tarzoma ko firgici a tsakanin al’umma.

0 Comments:
Post a Comment