Kafafen yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa sojojin ƙasar sun lalata wasu “jiragen Amurka” a lokacin da suke ƙoƙarin ceto matukin jirgin da Rundunar sojin Iran ta harbo, inda suka bayyana lamarin a matsayin babbar nasara.
Lamarin ya fara ne bayan Iran ta harbo wani jirgin yaƙin Amurka samfurin F-15 a sararin samaniyarta a ranar juma'a, Inda matukin yayi batan dabo.
Daga bisani, Amurka ta kaddamar da wani farmakin ceto mai haɗari, inda aka tura jami’an runduna ta musamman tare da jiragen sama domin nemo matukin da ya ɓace.
Sai dai a nata bangaren Iran ta sanar da bayar da tukuci mai tsoka ga duk Wanda ya bayyana ko Kuma ya sanar da Inda matukin ya boye.

0 Comments:
Post a Comment