Aƙalla mutane Bakwai ne Suka rasa ransu Sakamakon harin 'yan ta’adda a wasu Coci a jihar Kaduna.

Aƙalla mutane Bakwai ne Suka rasa ransu Sakamakon harin 'yan ta’adda a wasu Coci a jihar Kaduna.

Aƙalla mutane bakwai ne aka bayar da rahotan sun rasu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wasu coci guda biyu a ƙauyen Ariko dake Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, a yau Lahadi, 5 ga Afrilu, yayin da Kiristoci ke murnar bikin Ista.

Shugaban ƙungiyar wakilan kauyen Awon, wanda ƙauyen Ariko ke ƙarƙashinsa, Mark Bawa, ya tabbatar da harin ga manema labarai, inda ya ce cocin da abin ya shafa sune First ECWA Church da St. Augustine Catholic Church, duk a kauyen Ariko.

Ya ƙara da cewa rashin kyakkyawan sadarwa a yankin na iya ba ‘yan ta’addan damar kai harin ba tare da an yi saurin daukar mataki ba.

“‘Yan ta’addan sun zo da yawa ne. Inda suka kewaye yankin sannan suka fara harbin kan mai uwa da wabi. Mutane da dama ne suka mutu, wasu kuma an kai su cikin daji,” in ji shi.

Wannan harin ya faru ne daidai mako guda bayan wasu da ake zargin ‘yan ta’addan daji ne suka kai hari a ƙauyen Jos lokacin bikin Ranar Palms, inda sama da mutane ashirin suka rasu.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: