Fira ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya zargi ƙasar Sifaniya da nuna ƙiyayya da tsananin adawa ga Isra’ila, a yayin da rikicin diflomasiyya ke ƙara ƙamari tsakanin ƙasashen biyu.
Netanyahu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa bayan Isra’ila ta ɗauki matakin takaita shigar wakilan Sifaniya cikin wani cibiyar haɗin gwiwa da Amurka ke jagoranta a Kiryat Gat, wanda ke da alaƙa da shirye-shiryen da suka shafi zaman lafiya da taimakon jinƙai a Gaza.
Rahotanni sun nuna cewa an cire wakilan Sifaniya daga cibiyar bayan Isra’ila ta zarge su da yawan bayyana matsayi da maganganu da ke adawa da ƙasar. Netanyahu ya ce ƙasashen da ke adawa da Isra’ila ba za su samu damar shiga cikin shirye-shiryen tsaro da cibiyar ke kokarin samarwa ba.
Dangantaka tsakanin Sifaniya da Isra’ila ta ci gaba da tabarbarewa a ‘yan shekarun nan, musamman bayan Sifaniya ta amince da kafa ƙasar Falasdinu da kuma sukar ayyukan sojin Isra’ila a Gaza. Wannan ya haifar da ƙarin takun-saka, ciki har da janye jakadu da takaita hadin gwiwa a wasu fannoni.
Sifaniya kuwa ta ci gaba da kare matsayinta, tana cewa manufofinta sun ginu ne bisa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma la’akari da batun jinƙai, yayin da Isra’ila ke zargin ta da nuna bangaranci.
Wannan sabon rikici na ƙara nuna tsanani a dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu a cikin yanayin rikice-rikicen da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment