Ƙasar Mali ta sanar da cewa za a gudanar da faretin girmamawa a lokacin jana’izar marigayi Ministan Tsaro, Sadio Camara, wanda aka kashe a wani harin da 'yan tawayen ƙasar suka kai gidansa.
Mahukunta sojin ƙasar sun bayyana cewa za a yi jana’izar ne a yau Alhamis a wani sansanin soja da ke birnin Bamako, inda za a yi fareti na girmamawa kafin binne gawarsa.
Ana sa ran Shugaban ƙasa, Assimi Goita, zai halarci jana’izar, wadda za a gudanar cikin tsauraran matakan tsaro.
Rahotanni sun ce Camara mai shekaru 47 ya rasu ne bayan wani ɗan kunar bakin wake ya tayar da mota mai bam a gidansa da ke Kati, bayan kazamin artabu tsakanin sojoji, ‘yan tawayen Tuareg da kuma ‘yan ta’adda.
A jawabin da ya yi ga al’umma, Shugaba Goita ya bayyana marigayin a matsayin jarumin soja, yana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga ƙasar. Gwamnatin ta kuma ayyana kwanaki biyu na makoki na ƙasa domin girmama shi.

0 $type={blogger}:
Post a Comment