Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da bayar da tallafin Naira biliyan 2 ga waɗanda hare-haren ta’addanci suka shafa a ƙaramar hukumar Jos ta arewa.
Shugaban ya kuma bukaci shugabannin jihar Filato da su haɗa kai wajen warware rikice-rikicen da ke faruwa, tare da ɗaukar matakan da za su tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai da sulhu domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment