Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Juma’a, 1 ga watan Mayu, a matsayin ranar hutu domin bikin ranar Ma'aikata na wannan shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnati. A cikin wata sanarwa da Sakatare na dindindin a ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar, ministan ya taya ma’aikatan Najeriya murnar wannan rana.
Ya yaba da ƙoƙarin ma’aikata da sadaukarwarsu wajen ci gaban ƙasa, yana mai jaddada cewa gudunmawar su na da matuƙar muhimmanci ga bunƙasar Najeriya. Haka kuma ya bukaci ma’aikata su rungumi kishin ƙasa, ƙwazo, da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu domin samun ci gaba mai ɗorewa.
Gwamnatin ta kuma sake jaddada kudurinta na inganta walwala da tsaron ma’aikata tare da samar da yanayi mai kyau don bunƙasar tattalin arziki.
Ministan ya kuma bukaci ‘yan ƙasa su kasance masu zaman lafiya da bin doka, tare da ƙarfafa su su yi amfani da wannan lokaci wajen tunani kan muhimmancin haɗin kai da aiki tukuru wajen gina ƙasa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment