Majalisar Kansiloli 10 ta ƙaramar hukumar Kura ta bukaci Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Rabi'u Abubakar Sulaiman Babina, da Mataimakinsa, Hon. Bello Gambo Kura, su bayyana a zauren majalisar domin kare kansu kan zargin fitar da kudi sama da naira miliyan dari biyu (₦200m) ba tare da sanar da majalisar ba.
Majalisar ta yi gargadi cewa duk wasu bayanai da suka shafi kudi da aka fitar ba tare da amincewar ta ba za su zama abin bincike, kuma tana sa ran shugabannin za su yi cikakken bayani kan yadda aka gudanar da kudaden.
Source: Express Radio Nigeria.

0 Comments:
Post a Comment