Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Déby Itno, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da haɗin gwiwar ƙasashen biyu.
Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta fi mayar da hankali kan ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da kuma inganta tsaro a yankin Tafkin Chadi, inda ake fama da hare-haren ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
Shugabannin biyu sun kuma tattauna kan hanyoyin ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da tattalin arziki, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin ƙasashen yankin domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Ziyarar shugaban na Chadi na daga cikin ƙoƙarin ƙasashen Afirka ta Yamma da Tsakiya na ƙara haɗa kai wajen magance matsalolin tsaro da kuma bunƙasa ci gaba a yankin.
News Translation in English Language.
Tinubu Hosts Chadian President in Abuja for Talks on Security, Cooperation.
ABUJA, April 2, 2026 — Nigerian President Bola Ahmed Tinubu on Thursday hosted Chadian President Mahamat Idriss Déby Itno at the Presidential Villa in Abuja for high-level talks focused on security and bilateral cooperation.
The meeting centered on strengthening joint efforts to combat terrorism and insurgency in the Lake Chad region, where countries continue to face threats from armed groups.
Both leaders also discussed ways to deepen diplomatic and economic ties, emphasizing the importance of regional collaboration in promoting peace, stability, and development.
The visit underscores ongoing efforts by West and Central African nations to enhance cooperation in addressing shared security challenges and advancing regional integration.

0 Comments:
Post a Comment