Wata Babbar Kotun Tarayya ta amince da bayar da beli ga tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a kan kudi Naira miliyan 200, sai dai har yanzu yana tsare a hannun hukumar ta ICPC har sai ya cika sharuddan belin.
Sharuddan Belin:
Kotun ta gindaya wasu tsauraran sharudda kafin a sako shi, ciki har da:
Samar da mutane biyu da za su tsaya masa masu kima iri daya da belin.
Daya daga cikinsu dole ne ya kasance babban jami’in gwamnati mai matsayi a matakin aikin gwamnati (Grade Level 15 ko sama da haka)
Na biyun kuma ya zama fitaccen basarake.
Sannan dukkan su su mika fasfo dinsu ga kotu.
Duk da amincewa da belin, Nasir El-Rufai ba zai samu ‘yanci ba har sai an tabbatar da wadanda za su tsaya masa Sannan kuma sai an kammala dukkan takardun da ake bukata,
tare da cika dukkan sharuddan da kotu ta gindaya..
Ana tuhumar Nasir El-Rufai da laifuffuka da suka hada da:
cin zarafin ofis
badakalar kudi
zargin almundahana da karkatar da kudade.
Hukumar ICPC ce ta gurfanar da shi a gaban kotu, har zuwa lokacin da ya samu belin.

0 Comments:
Post a Comment