An tsaurara matakan tsaro a yayin taron ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da ke gudana a Abuja, inda ake sa ran wakilai sama da 7,000 za su halarta domin zaɓen sabbin mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC).
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sanda da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun baza jami’ansu a wurin taron, tare da aiwatar da cikakken bincike ga mahalarta, ciki har da wakilai da ‘yan jarida, domin tabbatar da tsaro.
Haka kuma, an girke motocin sintiri da jami’an tsaro a wurare daban-daban na harabar taron domin dakile duk wata barazana ga zaman lafiya yayin gudanar da muhimmin taron.
Taron na da matuƙar muhimmanci ga jam’iyyar, domin za a zaɓi sabbin shugabanni da za su jagoranci harkokin ADC na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.
Sai dai, wannan taro na gudana ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar rikicin shugabanci, inda bangarori daban-daban ke ikirarin halascin jagoranci. Rikicin ya kai ga shari’a a kotu tare da jawo saɓani da hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC.
Duk da waɗannan ƙalubale, shugabannin jam’iyyar sun jaddada aniyarsu na ci gaba da gudanar da taron kamar yadda aka tsara, tare da fatan samar da sabuwar shugabanci mai ƙarfi da haɗin kai.

0 Comments:
Post a Comment